Wasu Hausawa mazauna yankin da suka zanta da Muryar Amurka sun ce babu wata matsala da suke huskanta sakamakon wannan rikici da yayi sanadiyar mutuwar wani manomi mai suna Atu Anya. Mallam Adamu Datti, dan kasuwa a birnin Awka, yace suna gudanar da kasuwancinsu kamar yanda suka saba.
Alhaji Gidado Sidiki shine shugaban kungiyar Miyetti Allah a yankin kudu maso gabashin Najeriya kuma yace a wani lokaci kungiyar ta samu korafi daga manoman yankin cewar makiyaya na lalata gonaki kuma sun yi kokarin sasanta wannan al’amari, amma jin aukuwar wannan rikici, kungiyar zata gudanar da nata bincike.
Jami’an tsaro suna bakin kokarinsu su gano wadanda suka aikata wannan danyen aiki domin doka tayi aiki a kansu. Mallam Garba Umar shine kwamishinan yan sandan jihar Anambara, yace rundunar 'yan sanda tana gudanar da bincike a wannan batu sai dai yace ya zuwa yanzu babu wani karin bayani kan lamarin.
Your browser doesn’t support HTML5
ANAMBRA