Ana Jinjinawa 'Yan Kato da Gora, da Maharba da Suke Fafatawa da 'Yan Bindiga
‘Yan sintiri da Mafarauta, rike da bindigogi sun taru kofar fadar Sarki a Maiduguri, 4 ga Satumba 2014.
'Yan kato da gora da kuma mafarauta ne da suka sami goyon bayan jami'an tsaro suka kwato garuruwan Mubi da kuma Maiha.
WASHINGTON, DC —
Yanzu haka rahotanni daga jihar Adamawa,arewa maso gabashin Najeriya na cewa dakarun kasar dake samun tallafin maharba,da kuma yan kato dagora, wato civilian JTF na cigaba da samun nasara a fafatawan da suke yi da maharani Boko Haram a yankin Gombi.
Tun bayan kai hari garuruwan Mubi da Maiha ne, mayakan Boko Haram da daman gaske ne suka gudo zuwa Hong da Gombi,inda suka wuni harbe-harbe kamun maharba su kawo dauki.
Ga karin bayani da Ibrahim Abdulaziz ya aiko mana.