ABUJA, NIGERIA - Ganin yadda komai yake kokarin tsayawa cak a Najeriya a batun tattalin arziki da hada-hadar kasuwanci, na ji ta bakin manazarta da masu fashin baki.
Ana Fafutuka Da Tafka Dambarwa A Gaban Bankunan Najeriya
Dr. Farouk Bibi Farouk, Masanin kimiyyar siyasa a jami’ar Abuja, ya ce rashin kyakyawan tsari na canjin kudin ka iya haifar da matsaloli a kasa.
Da nake jin ta bakin wasu ‘yan kasar, sun bayyana irin kalubalen da suke fuskanta da yadda canjin kudin ya shafi rayuwarsu ta yau da kullum.
Tun da aka fara batun sauya launin takardar naira irin labaran da ake cin karo da su kenan a kafafen yada labaru na kasar.
Ana Fafutuka Da Tafka Dambarwa A Gaban Bankunan Najeriya
Sakamakon hakan ne dai yasa wasu gwamnonin arewacin Najeriyar suka yi karar gwamnatin kasar a kotu.
A daidai wannan lokacin ne kuma kotun kolin kasar ta ce ta dakatar da wa’adin daina amfani da tsofaffin kudin har sai ta gama sauraron ba’asin masu shigar da kara.
Saurari cikakken rahoto daga Hauwa Umar:
Your browser doesn’t support HTML5
Ana Fafutuka Da Tafka Dambarwa A Gaban Bankunan Najeriya.mp3