Taron da aka yiwa take da karfafa hadin gwiwan Sojoji,domin tabbatar da zaman lafiya, da daidaito da kuma ci gaba, ya yabawa tsohon shugaban janar Samaila Bakayoko, na kasar Cote d’Ivoire.
Wakilan taron sun jinjinawa, tsohon shugaban masamman wajen rawar da ya taka na sasanta rikicin kasar Mali.
Taron yayi tsokaci kan cutar Ebola, da bada tabbaci taimakawa ta duk inda ya dace domin ganin cewa an shawo kan cutar.