An Shirya Taron Sulhu Tsakanin Matasa a Jihar Flato
Jos
Rundunar ta musamman dake aikin tsaro da zaman lafiya a jihar Flato ta shirya taro tsakanin matasa a kudancin jihar Flato.
Da yake jawabi a bikin bude taron, kwamandan rundunar tabbatar da zamaan lafiya a jihar, Manjo janar Henry Ayola, ya shawarci matasan da su gafartawa juna.
Kamar yadda wakiliyarmu a yankin Zainab Babaji ta aiko, yankin kudancin jihar da ya kunshi kananan hukumomi shida sun fuskanci matsaloli da suka hada da kisa, da sace sacen dabbobi, da kone konen gidaje.