Mazauna karamar hukumar Mubi na zaman dar-dar sakamakon harin da wadansu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai gidan shugaban kasaramar hukumar karo na biyu. Sai dai shugaban karamar hukumar ya tsallake rijiya da baya, domin baya gida a daidai lokacin da ‘yan bindigan suka kai harin.
Wakilinmu Ibrahim Abdul’aziz ya ruwaito cewa, sau da dama dai ana danganta irin wadannan hare haren da ‘yan fashi da makamai.