AGADEZ, NIGER - Taron ya hada kungiyoyin agaji na kasa da kasa da abokan hulda da kuma masana domin bayar da shawarwari kan yadda za a inganta sha’anin ilimin karkara a kasar Nijar.
Taron Habaka Ilimi Na Karkara A Nijar
Karancin kwararrun malamai da rashin ingantattun dakunan karatu a karakara da nisan makarantu a galibin yankunan karkara na daga cikin matsalolin da aka yi nazari akansu yayin babban taron na bunkasa ilimi domin samun mafita.
Taron Habaka Ilimi Na Karkara A Nijar
Fannin ilimi na kan gaba a jerin ayyukan da Shugaban kasar Nijar Bazoum Mohamed ya yi alkawarinn fifiko a tsawan wa’adin mulkinsa domin acewarsa duk wani ci gaba bazai samu ba sai da ilimi, to sai dai rashin baiwa yaran karkara ilimi na yiwa kudirin Shugaban tarnaki; mafari kenan da hukumomin Nijar suka gudanar da babban taro don bunkasa ilimin yankunan karkara.
Taron Habaka Ilimi Na Karkara A Nijar
Taron kuma ya mayar da hankali ne kan samar da hanyoyin tallafawa da ilimantar da kananan yaran karkara.
“Za mu mayar da hankali ne wajen neman hanyoyin bunkasa ilimi yara don mun lura da irin rikon sakainar kashin da muka yi na ilimi a yankunan karkara, shi ne babbar matsalar da ke hana mu ci gaba saboda haka muke son samun mafita kuma mafitar ita ce samar da ingantaccen tsarin da zai kula da harakar ilimi musan a yankunan karkara” In ji Mohamed Anako, shugaban Majalisar jihar Agadas.
Taron Habaka Ilimi Na Karkara A Nijar
Koma bayan ilimin yaran karkara wata matsala ce da ke hana ruwa gudu a kokarin ilmantar da al’umar kasar saboda haka masana irin su Alhaji Labo ke ganin wannan taron wata hanya ce ta bunkasa ilimi a Nijar, na taron da ya hada kungiyoyin agaji na kasa da kasa da masu hannu da shuni da masana inda suka bayar da shawarwari kan yadda za’a inganta ilimi a yankunan na karkara.
Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmoud:
Your browser doesn’t support HTML5
An Kammala Taron Habaka Harkar Ilimi A Yankunan Karkara A Nijar .mp3