Wasu 'yan gudun hijira da suka arcewa daga garuruwansu a saboda hare haren 'yan Boko Haram.
Wata hukumar farar hula da ake cewa Civil Defense ta gano wani wurin da ake karkata akalar kayyakin agaji.
WASHINGTON, DC —
Hukumar farar hula ta Civil Defense a jihar Gombe, arewa maso gabashin Nigeria, ta gano wani wuri da ake amfani da shi wajen karkata akalar kayayyakin agaji da gwamnatin taraiyar Nigeria take aikowa da shi domin a rarrabawa yan gudun hijira a arewa maso gabashin Nigeria.
Wakilin sashen Hausa Abdulwahab Mohammed ya aiko da rahoton, cewa bincike na nuni da cewa kayayyakin agajin, ana ajiye wa ne a baban wurin ajiye kayyakin da hukumar NEMA ta samar, wanda daga baya ake rabawa a matsayin kayan tallafi.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5
An Kame Mutane Bakwai a Gombe, a Saboda Suna Karkata Akalar Kayayyakin Agaji - 3'16"