Kungiyar kwadago ta duniya ta fidda rahoton dake bayani cewa a duniya baki daya akwai kimanin yara miliyan 168 yan shekaru biyar zuwa 14 da suke aikin kwadago wanda daga ciki yara miliyan 15 a najeriya suke wanda hakan na nuni da cewar kasar itace ke da mafiya yawa a kasashen Afrika ta yamma.
Wasu yaran sun fadawa wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka a Bauchi, cewar idan mutum na sana’a yafi, saboda a sana’ar da suke yi suna samun Naira dari uku ko dari biyu ko kuma kasa da hakan. Wani yaron yace Mahaifinsa ne ya kaishi koyon dinky kuma a wannan aiki yana samun dana bin kashewa.
Shugaban shiyar Arewa maso gabacin Najeriya ta kungiyar kare hakkin mata da yara ta Women’s Situation Room tace yara dayawa da suka rasa iyayensu ko kuma daya daya a cikin iyayen suna zaune kara zube, sune ake turawa suje su kawo abin da za a ci kuma hakan ne ke kai ga fadawan kananan yara a cikin ayyukan kwadago wani lokacin ma har a ci zarafinsu.
Shugaban Kungiyar Women’s Situation Room tace gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu suna alhakin samarwa yaran gidajen marayu inda za a kai irin wadannan yara ana kula da su ba sai sun je waje neman kudi ba.
Your browser doesn’t support HTML5
An gudanar da bukin ranar yaki da bautar da kanana yara ta duniya