Cohen ne ya dauki hirarsu a asirce a cikin watan Satumban shekara 2016, yayin da Trump ke takarar neman shugabancin kasa. Lauyan Cohen Lanny Davis ne ya baiwa CNN wannan faifan.
Trump ya sha musunta wannan batun neman mai yiwa kamfanin Playboy talla, Karen McDougal, wacce ta sai da labarinta ga wani kamfanin buga jarida American Media a kan dala dubu 150. Sai dai babu wani labari da aka buga game da alakarsu.
A cikin takaitacciyar muryar da aka dauka, an ji Cohen na fadin, muna bukatar mu bude wani kamfani da zamu tura duk wasu bayanai game da abokin mu David, wato akwai yiwuwar yana nufin abokin Trump kuma shugaban ma’aikatar buga labarai ta American Media David Pecker.
A cikin watan Afrilu, hukumar binciken manyan laifuka ta FBI ta kai samame a ofishin Cohen inda ta kwace faya fayai da dama da aka aikesu ga lauyoyin tarayya.
Trump dai ya bayyana rashin jin dadinsa kan bincike da ake yiwa Cohen.