Amurka Ta Ce Akwai 'Yan Hezbollah a Venezuela

Sakataren harkokin waje Amurka, Mike Pompeo,

Da aka tambaye shi ko yana ganin akwai hannun Rasha a rikicin siyasar kasar ta Venezuela? sai ya ce, komai mai yiwuwa ne, mun ga abin da ta yi, saboda haka, ya kamata mu zauna cikin shirin domin abin da ka iya faruwa a nan gaba.

Kwamandan rundunar dakarun Amurka da ke kudancin kasar, ya tabbatar da ikrarin da Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo ya yi na cewa, akwai alamun mayakan Hezbollah a kasar Venezuela.

Amma ya ce a halin da ake ciki a yanzu, dakarun Amurka sun fi maida hankali ne wajen ganin sun tsare lafiyar Amurkawa da kuma kokarin tallafa musu, saboda mawuyacin halin da suka shiga.

Kwamandan dakarun na Amurka, Navy Admiral Craig Faller, ya fadawa manema labarai a karshen makon da ya gabata cewa, Amurka na iya bakin kokarinta wajen ganin duk ‘yan kasarta da dukiyoyinsu da jami’an diplomasiyya da ke kasar ta Venezuela, sun samu cikakken tsaro.

Da aka tambaye shi ko yana ganin akwai hannun Rasha a rikicin siyasar kasar ta Venezuela? sai ya ce, komai mai yiwuwa ne, mun ga abin da ta yi, saboda haka, ya kamata mu zauna cikin shirin domin abin da ka iya faruwa a nan gaba.

Matsalar da tattalin arzikin Venezuela ya shiga, ya sa shaguna da dama sun kasance wayam, yayin da miliyoyin ‘yan kasar suka bazama wasu kasashe domin neman hanyoyin kyautata rayuwarsu.