ABUJA, NIGERIA - Wata sanarwa da kakakin hukumar DSS na kasa DR. Peter Afunyaya ya aikewa sashin Hausa na Muryar Amurka na cewa jami'an tsaron sun cafke Abubakar Muhammad da ake kira Abubakar Direba, da makamai da harsasai manya har guda dari hudu da tamanin da shida, abubuwan fashewa ashirin da hudu, da kudade a cikin wata mota kirar Gulf.
Bindigogin da aka samu lokacin kama Abubakar Muhammad aka Abu Direba - mai safarar miyagun makamai
Bugu da kari, cikin aikin na hadin gwiwa, jami'an tsaron sun kuma kai wani samame a maboyar jagoran ‘yan ta'addan nan na jihar Kogi mai suna Kabir Bala da ake yiwa lakabi da Okwo.
Dan ta'addan da sauran mutanensa sun budewa jami'an tsaron wuta inda nan take su ma suka maida martani har daga karshe suka bindigeshi.
Harsasai da aka cafke daga wurin buyar Abubakar Direba mai safarar miyagun makamai
Bindiga da aka samu lokacin kama Kabir Bala aka Okwo - Jagoran ‘yan ta’addan Jihar Kogi
An sami babbar bindiga kirar Ak 47, da wasu bindigogi na gargajiya guda shida, wayoyin salula da layu da wasu sauran abubuwa.
Layu da wasu tarkace da aka samu lokacin kama Kabir Bala aka Okwo - Jagoran ‘yan ta’addan Jihar Kogi
Hukumar tsaro ta DSS ta nemi jama'a musamman masu mu'amala da wuraren hada-hadar jama'a kamar kasuwanni da shaguna da su rika yin kaffa-kaffa da takatsantsan, sannan su sa ido kuma su kai rahoton duk wani motsi da basu yarda da shi ba ga jami'an tsaro.