Mai Tambaya Mai Nasara Nasarawa Funtua ya bukaci sanin abin da ya sababa rikicin Sudan da kuma yadda za a iya magance yawan rikice rikice a kasar ta Sudan. Sai kuma tambayar Malam Aminu Malam Madori Jihar Jigawa a Najeriya, wanda ya bukaci bayani daga masana akan dalilan dake sa wasu kasashe a kuryar Afirka da ma wasu sassa a kasar China dake yankin Asiya, a lokacin da wasu kasashen duniya ke fama da ambaliyar ruwa.