Wata fashewa a wani masallaci dake kauyen gadan, na karamar hukumar gezawa ta jihar kano ya raunata kimanin mutane 35, a yau laraba. Al’amarin ya faru ne da misalin karfe 5 da mintuna 20 na safiya yayin sallar asubahi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, yace sakamakon binciken farko-farko ya nuna cewar man fetur ne ya sabbaba fashewar.
Masallacin da wani matashi ya cinna wa wuta a Larabar Abasawa
An kuma kama wanda ake zargi da haddasa fashewar, mai suna Shafi’u Abubakar mai shekaru 38 da haihuwa.
Masallacin da wani matashi ya cinna wa wuta a Larabar Abasawa
An ruwaito kiyawa yana cewar, “a bayanin daya baiwa ‘yan sanda, wanda ake zargin ya bayyana wata dadaddiyar takaddamar rabon gado a matsayin dalilnsa na haddasa fashewar. a cewarsa, “ya aikata aika-aikar ne domin nuna adawa da wata dadaddiyar takaddamar danginsa akan rabon gado, kuma yayi haka ne domin a saurare shi.”
HOTUNA: Masallacin Da Wani Matashi Ya Cinna Wa Wuta A Kano
Ya cigaba da cewar, “rundunar ‘yan sandan jihar kano na baiwa al’umma tabbacin cewar ana gudanar da cikakken bincike akan lamarin kuma za’a fitar da bayanai anan gaba. a halin yanzu wanda ake zargin na hannun ‘yan sanda, kuma za’a gudanar da cikakken bincike akan lamarin.”
Masallacin da wani matashi ya cinna wa wuta a Larabar Abasawa