Donald Trump ya biya diyyar dala miliyan biyu a matsayin wani ɓangare na sasanta takaddamar yin amfani da tsohuwar gidauniyyarsa, wajen cimma manufofinsa na siyasa da kasuwanci.
An zargi Trump da yin amfani da kudaden gidauniyar don biyan kudaden wasu kararraki, da kuma tallata gidajen otel dinsa masu suna Trump, da kuma kashe kudaden wajen biyan bukatun kansa – kamar siyan wani zanen hotonsa da ya sa a wajen shakatawarsa.
Sannan an rarraba dala miliyan biyu daidai ga wasu kungiyoyin agaji takwas, waɗanda suka haɗa da Giduniyar Taimakon Yara wato Children’s Aid Society, da Asusun Kwaleji na United Negro da Gidan Tarihin Holocaust na Amurka, a cewar wata sanarwa da Babban lauyan New York Letitia James ta fada.
An biya wadannan kudade ne ranar guda da 'yan jam'iyyar Democrat a majalisar wakilai suka gabatar da wasu tuhume-tuhume guda biyu na tsige shugaba Trump, wani muhimmin mataki da ke nuna cewa ya yi amfani da mukaminsa don biyan bukatun kansa, kuma ya cancanci a cire shi.
A yanzu haka Trump yana fuskantar matsaloli na shari'a da ke ci gaba ta fuskoki da dama.
-AFP