An Fara Amfani Da Motocin Sufuri Masu Tuka Kansu A Kasar Paris!

Motar Sufuri Mai Amfani Da Hasken Rana

Hukumomi a kasar Paris, sun kaddamar da motocin sufuri, masu tuka kansu, kuma da amfani da hasken rana. Wadannan motocin dai an samar da su ne, a yunkurin rage cunkoso na abubuwa hawa, da kawo karshen cututuka dake yaduwa a sanadiyar hayakin motoci, a manya-manyan garuruwan kasar.

Wadannan sababbin motocin masu suna “EZ10” suna amfani da kyamarori, dake nuna musu wajen zuwa, lokacin tafiya, da hanyoyin da suka kamata subi.

A karon farko motocin sun dauki mutane, da tafiyar ta kai mitoci dari da talatin, don zuwa wasu yankuna a babban birnin Gare de Lyyon zuwa birnin Austerliyz, wanda yake da cunkoson mutane. A shekara mai zuwa ake sa ran kara yawan garuruwan da motar zata dinga zuwa.

Wadannan motocin sufurin na daukar mutane da yawa ne, don a rage yawan motoci a kan tituna, kana suna amfani da hasken rana, wanda baza su kawo hayaki da ke haifar da cuttutka da suka hada da mura, tari, ciwon ido, da dai wasu cuttutuka da kan iya zama babbar barazana ga lafiya mutane.