Gungun kwararrun masana kimiyyar na’ura mai kwakwalwa da lauyoyi na kasar Amurka sun bukaci ‘yar takarar shugabancin Amurka a karkashin jam’iyyar Democrats Hillary Clinton, wadda tasha kaye a hannun abokin takararta na jam’iyyar Republican Donald Trump, ta nemi a sake kidaya kuri’un da aka jefa domin a cewar su, sun lura da wasu abubuwa da suka saba wajan kididdigar kuri’un a wasu jihohi.
J. Alex Haldeman, masanin kimiyyar na’ura mai kwakwalwa ya bayyana cewa na’urorin zaben nada matsalolin tsaro na yanar gizo da ka iya ba masu kutsen satar bayanai damar yin kutse.
Ya jaddada cewa a yanzu haka babu tabbacin alamun yin kutse a na’urorin zaben a wasu jihohin da zababben shugaban Amurka Donald Trump ya sami nasara. Amma duk da haka ya zama wajibi a kidaya su hannu da hannu domin tabbatar da ba a yiwa na’urorin kutse ba.
Da farko mujallar New York, ta bayyana rade radin tangardar na’urorin zaben a Wisconsin, da Michigan, da kuma Pennsylvania da suka bada sakamakon da suka sabawa juna lamarin da baiwa Clinton dadi ba.
Kididdiga ta nuna cewa a Wisconsin, Hillary Cliton ta sami karancin kuri’u da kashi bakawai cikin dari a wasu kananan hukumomi da suka dogara kan na’urorin zaben idan aka kwatantasu da wasu kananan hukumomin da suka yi amfani da takarda da tawadar zabe. Dangane da wannan binciken, ya nuna cewar an hana Hillary kusan kuri’u 30,000 kenan.