Kai Ma Ka Dara

Wata rana wasu jami'an 'yan sanda suna sintiri akan hanya, sai kwatsam suka ga wani dan kwaya yana tafiya a gefen hanya, kamar dai yadda suka basa yi a bakin aiki, sai daya daga cikin su ya yi masa tambaya, Malam ina zaka cikin daren nan?

To abin ka da mashayi, su basu gane cewar ga irin halin da yake ciki ba, sai kawai amsa masu ya ce, "aiki zani". aiki a cikin daren nan? inji jami'an tsaron, sai ya ce haka.

Abin sai ya basu mamaki, sai daya daga cikin su ya ce, malam a ina kake aiki da zaka fito a irin wannan lokaci haka? sai ya kada baki ya ce, "a gidan radio nake aiki".

Da jin haka sai daya daga cikin su ya ce masa, malam ai yanzu ko ma'aikatan gidan radio sun tashi daga aiki, budar bakinsa sai ya ce masu, ai ni aiki na shine idan an tashi nike yin shuuuuuu! wato a nufin sa idan an rufe tashar radio, yadda take iska shhhhhh! a nufin sa irin aikin da yake yi masu kenan

Your browser doesn’t support HTML5

Kai Ma Ka Dara