Idris Adamu Ya Soki Amaju Pinnick Kan Rashin Isassun Kudin Tikitin Jirgi Da Wuraren Kwanan 'Yan Super Eagles

Tsohon mai kula da harkokin tallace tallace a karkashin ofishin hukumar kwallon kafa ta Najeriya Malam Idris Adamu, ya soki shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya Amaju Pinnik a sakamakon korafin da yayi na cewa hukumar bata da isassun kudade da zata dauki dawainiyar biyan kudaden jigilar ‘yan wasan kungiyar Super Eagles kasar Zambiya ranar lahadi mai zuwa inda zasu fafata wasan neman shiga gasar cin kofin duniya na shekarar 2018.

A ranar talatar data gabata ne Pinnick ya bayyanawa kwamitin dake kula da harkokin wasannin kwallon kafa cewar har yanzu basu niya kudaden jigila da wuraren kwanan ‘yan wasan a birnin Ndola ba a sakamakon rashin isassun kudade.

Adamu, yayin da yake mayar da martani ya yi ikirarin cewa furta irin wadannan kalaman tamkar zamba ce.

Ya kara da cewa akwai makudan kudade a asusun hukumar kwallon kafa ta Najeriya da sashen tallace tallace Pamodzi, wadanda a cewar sa zasu isa a dauki dawainiyar dukkan bukatun ‘yan wasan.

Ya ce “yawancin masu daukar nauyin wasannin kungiyar sun biya, kamfanin Emzo Paracetamol, da Glo duk sun biya, kuma akwai kudi dala miliyan guda daga Super Sport da fannin tallace wanda kashi ashirin cikin dari kacal za’a cire na kamisho, sa’annan a ba hukumar kwallon kafa ta Najeriya sauran.

Adamu ya kara da cewa ya samarwa da hukumar kudi naira biliyan 1.4 a shekara yayin da yake aiki da hukumar kafin Pinnick ya tumbuke shi.