Dan Shekaru "20" Ya Zama Zakaran Gwajin Dafi Na Kurame!

Safar Hannun Don Magana

Fasahar Navid Azodi, wani dalibi mai shekaru ashirin 20, da haihuwa tazama zakaran gwajin dafi. Shi dai wannan dalibin haifaffen kasar Amurka ne, amma iyayen shi ‘yan asalin kasar Iran ne, wanda iyayen shi suka dawo kasar Amurka don samar mishi rayuwa mai inganci.

Tun bayan haihuwar shi yayi fama da matsalar rashin iya magana, wanda har yakai shekaru bakwai 7, baya iya magana. Daga bisani likitocin shi sun bayyanar da cewar ba zai iya magana ba arayuwar shi.

Hakan dai yasa shi ya iya magana irin ta kurame, da yake amfani da hannun shi wajen bayyanar da abun da yake so. Hakan yasa shi tunanin yadda sauran mutane suke samun matsaloli wadanda basu iya magana.

Yanzu haka ya samu damar lashe lambar kyautar Lemenson ta jami’ar farko a duniya, a fannin kimiyya da fasaha Masachuset Institute of Technology. Shi dai ‘yaron yana jami’ar Washington, inda ya kirkiri wata safar hannu da ake amfani da ita, wajen magana da hannu a inda ita kuma kwamfuta, zata rubuta abun da mutun yake cewa a rubuce. Hakan yasa ya samu kyautar dallar Amurka dubu goma $10,000 dai-dai da naira milliyan uku da dubu dari biyu.