A Gobe Lahadi Za'a Samu Karin Awa 1 A Agogon Kasar Amurka

A kasar Amurka da wasu kasashen yamma, sukan samu canjin lokaci sau 2 a shekara. A kan dai kira wannan canjin yanayin “Spring forward, fall back” a turance, wanda ma’anar ke nufin, lokacin yanayin sanyi dare na saurin yi, kuma akan samu dare mai tsawo, haka lokacin bazara rana kanyi tsawo.

Daga ranar 13, ga wannan watan na Maris, mutane a kasar Amurka da wasu kasashe na yamma, zasu kara awa daya a agogon su. Wanda idan kuma Allah, ya kaimu watan Nuwamba 6, ga wata sai a rage awa daya daga agogo. A takaice hakan na nufin cewar za’a samu ragin awa daya daga lokacin da ake da shi tsakanin kasar Amurka da Najeriya, inda za’a samu tazarar awowi 5 madadin awowi 6 a tsakanin da kasar Najeriya.

A dai-dai tsakanin lokacin da aka kara ko aka rage awa 1, ma’aikata ko ‘yan makaranta zasu samu karin awa 1, bayan tashi daga aiki kamun rana ta fadi. Wasu na ganin kamar wannan wata hanyace ta sa mutane su kara kashe kudi. Domin suna ganin kamar idan mutane suka tashi aiki suna ganin sauran rana zasu bukaci zuwa kasuwa da ma wasu gurare tunda rana bata faduwa da wuri balle su tafi gida. A dai-dai lokacin da zamu dinga kawo muku shirye shiryen mu na rana wanda zamu dinga fara da karfe 11:00 na safe madadin karfe 10:00 na safe a nan babban birnin tarayyar Amurka Gundumar Kwalambiya.