Amanda Toombs, mai shekaru 27, malama ce a wata makarantar firamari a jihar Carolina ta arewa, a nan kasar Amurka. Amanda, bata hada komai da aikin ta ba, domin kuwa daliban ta sune rayuwar ta. Tace ta sadaukar da rayuwar ta ga wadannan daliban da take kashe awowi dasu a kullun.
Saurayin Amanda Justin Coast, mai shekaru 31, kuma yakasance yana son ta matuka, amma ya rasa ta yadda zai fito mata ya gayama ta, yanason ya aure ta, don yasan wani abune mai wuya ne. Amma ya dade yana tunanin ya zaiyi, sai ya fito da wata dubara, wadda yaje makarantar da take koyarwa a dai-dai lokacin da take cikin aji.
Ya samu wani kyalle yayi rubutu cewar “Amanda kiyar da ki aure ni” sai yaba ma daliban ta suka rike suka shiga cikin aji, jim kadan sai gashi ya shigo cikin ajin, sai ya roketa da ta yarda zata aure shi, sai ya sakamata zoben alkawali. Amanda tace gaskiya wannan salon da ya fito da shi yayi dai-dai, domin kuwa koda bata son shi, hakan da yayi saboda kaunar da takema daliban ta zai sa ta so shi.
To samari taya kuke gabatar da kan ku ga ‘yan-mata, kuma ‘yan-mata me kuke tattaunawa tsakanin ku da kawayenku a kan samari? Ku rubuto muna a shafinmu na dandalinvoafacebook.com