Mawaki "Justin Beiber" Ya Wulakanta 'Yar Shekaru 16

A al’ada a kowace kasa ko al’ummah, akan samu wasu fitattu, kodai mawaka, ko ‘yan fina-finai, masu kudi, ko ‘yan siyasa, da za’aga cewar jama’a na son su. Wanda a wasu lokutta idan suka fito kowa zai so ya dauki hoto da su, ko suyi mishi rubutu a wata takarda.

Hakan yazama wani abun sha’awa ga masu son wadannan mutane, domin kuwa a wasu lokutta mutane kan nuna cewar ai sun taba haduwa da wani fittacce. Sanannen yaron nan mawaki "Justin Bieber", ya fito cikin jama’a, wata ‘yar karamar yarinya “Julia” mai shekaru 16, tana tare da yayarta “Randa”, ta nemi tayi hoto da mawakin, domin kuwa tana son shi.

Sun tunkari yaron don suyi hoto da shi, sai yace musu bazai yi hoto da suba, domin kuwa yayi hotuna sama da billiyoyi da mutane. Hakan dai ya jawo mishi bakin jini daga mutane da dama, domin kuwa ana ta sukan irin wannan halin na girman kai. Yarinyar kuwa ta furta cewar bata son shi, a dalilin wulakanci da yayi musu.