Aikin Malunta Sana'a Da Tafi Kowace Daukaka

Koyarwa na daya daga cikin sana’o’in da su ka fi kowanne wahalarwa, amma kuma albashin ta na daga cikin mafi karancin tsoka, musamman ma a kasashe masu tasowa kamar Nigeria. Wannan dalili watakila shine ya kawo maganar da mutane ke yawan fada na cewa, “rabon malamai sai a lahira”.

Duk da rashin biya mai kyau da kuma yanayi mara dadi da malamai ke fama da shi, wasu daga cikin su sun zabi su jajirce su sadaukar da kan su, abun da ke basu karfin guiwa shine ganin sun koyar tare da horar da daliban su zuwa wani matsayi mai girma.

Duk da irin al’adar da ta zama ruwan dare ga malamai, inda suke tashi daga wannan makaranta zuwa wata don neman karin albashi, an danganta wannan da irin gamsuwar da ake samu wajen ganin dalibai sun tashi daga wannan mataki zuwa wani mataki na ilimi, har su kai ga cimma cikakken burin su.