Matsalolin Rayuwa Basu Kamata Su Karyama 'Ya-Mace Gwiwa Ba

Fatima Rabiu

Daya daga cikin mataslolin da Farima Rabiu ta fuskanta su ne, a lokacin da take gida Najeriya, dukan harkokin ta na karkashin iyaye ta, amma yanzu da ta ke da yanchi, kuma da ta ke makaranta a wata kasar ta da ban, ba tare da iyayen taba, yanzu alhakin kula da kanta da kuma tsare mutunchin kanta na duk rataye a wuyan ta baki daya.

Bayan dukkanin wadannan matsalolin da ta tarar, hakan bai mata cikas ba a fannin samun nasarori akan abubuwan, da tasa a gaba ba. Muhimmi a cikin nasarorin da ta samu kuwa shi ne, samun takadar shedar gama karatun digiri na farko. Sakamakon wannan nasarar, shi ne ya dada kara mata karfin gwiwa domin cigaba da neman karin ilimi da kuma samun digiri na biyu wanda yanzu take shirin kammalawa.

Babban burin ta shi ne idan, ta gama karatun ta lafiya, da sakamako mai gamsarwa, Insha Allah, sannan kuma tana son ta koma gida Najeriya, tayi aure, sannan kuma ta sami aiki, domin yin amfani da ilimin ta wajen ingata rayuwan mutanen kasar. Ta kuma kara da cewar, ilimi shine gishirin zaman duniya, don haka idan har mace zata iya, to lallai yazama wajibi ga maza su tashi tsaye.