Kwari Sun Zama Abincin Wani Mutun! Ya kubuta Da Rayuwar Shi

Kwari

Wani mafarauci mai suna Reg Foggerdy, dan shekaru sittin da biyu 62, ya bar gidan shi da niyar zuwa cikin daji don farauta. Shi dai Mr. Reg, ya bar motar shi a bakin hanya, ya shiga daji da burin kamo Rakumin daji, a cikin wani daji mai yawan sahara, a yankin yamma a kasar Australia.

Dangin Mr. Reg, sun nemeshi na tsawon kwanaki shida 6, amma babu labarin shi, wanda daga bisani suka sanar da hukumomi don neman shi. A karshe dai an samu ganin Mr. Reg, a cikin kungurmin daji wanda ya kwashe kwanaki shida 6, babu ruwa balle abinci.

Iya tsawon kwananki shida da Mr. Reg yayi a cikin daji, yayi ta kama kwari yana ci a matsayin abinci. A dai-dai lokacin da aka same shi a bakin wata bishiya, baya ko iya motsi, domin kuwa ruwan jikin shi ya kare, yana kokarin mutuwa. Amma dai yanzu haka an dauke shi zuwa asibiti, kuma yana samun kulawa ta musamman.