Kwac din kungiyar kwallon kafa ta misira Hector Cuper ya ce kungiyar sa ta sha alwashin lashe duka maki uku a karawa ta biyu da kungiyar zata yi da Najeriya ranar talata a birnin Cairo.
Kungiyar ‘yan wasan ta yi kunnen doki da kungiyar Super Eagles a wasan su na farko da suka buga a filin wasan Ahmadu Bello Stadium dake jahar Kaduna.
Duk kungiyar da ta sami nasara kan takwarar ta a karawar da zasu yi a Alexandria, zata sami hayewa zuwa gasar cin kofin duniya na nahiyar Afirka da za’a buga a kasar Gabon.
A wata hira da kwac din a talabijin na Alexandria, ya bayyana cewa zasu shirya wasa mai kyau kuma suna sa ran samun nasara akan kungiyar Super Eagles ta Najeriya.
Ya ce “muna da abu guda da muke so mu samu wato nasara akan Najeriya, kuma duka ‘yan wasan mu a shirye suke kuma yanayin wasan na wannan lokacin zai canza ba kamar wasan mu na farko ba.