Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Fara Gasar NPFL 2016/2017 Ranar 14/1/2017 Tsakanin Kano Pillars Da Ifeanyi Ubah


A shirye shiryanta na fara wasan firimiya lig na tarayyan Najeriya 2016/2017, hukumar dake kula da wasanin lig lig ta Najeriya (LMC) ta tsayarda ranar Asabar 14/1/2017 a matsayin ranar da za'a fara fafatawa a wasannin Firimiya lig na kasar na shekarar 2016/2017 (NPFL) mako na farko.

Haka kuma hukumar tace za'a karkare wasannin a watan yuli na shekara ta dubu biyu da Goma Sha bakwai. Ga yadda wasan zasu kasance a satin farko

Ranar 14/1/2017 Kungiyar kwallon kafa ta Kano pillars zasu karbi bakuncin Ifeanyi Ubah.

A ranar Lahadi kuwa 15/1/2017, Kungiyar kwallon kafa ta Shooting Starts zasu fafata da Lobi.

MFM da Niger Tornadoes. Kungiyar kwallon kafa ta ABS zasu gwabza da Akwa United. Yayinda masu rike da kambun Enugu Rangers, zata marabci Abia Worrios.

Har ila yau kungiyar kwallon kafa ta River United, zasu kece raini da El-kanemi Warriors. Remo Start kuwa zasu buga da Plateau United. Katsina United da Gombe United. Eyimba zasu fafata da Sunshine, Wikki Tourist zasu kece raini tsakanunsu da Nasarawa United .

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG