Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Na Neman Wani Ma'aikacin Civil Defense Ruwa a Jallo


Nigeria civil defense
Nigeria civil defense

Hukumar ‘yan Sandan Jahar Sokoto,tana nema wani jami’in hukumar tsaro da kare lafiyar jama’a, wato “Civil Defense Corps” mai suna Aliyu Jekada, a bisa laifin dabbawa wani Kasimu Dandaba dan shekaru 25, wuka.

Wannan dai ya faru ne a garin Wamakko, hedkwatar karamar hukumar ta Wamakko, a tsakar dare biyo bayan wata ‘yar takaddama da ta shiga tsakanin su.

Kakakin rundunar ‘yan Sandan Jahar ta Sokoto, Sabo Kurawa wanda ya shaidawa kamfani dillanci labarai na Najeriya, afkuwar batun ya ce hukumar na biye da Aliyu Jekada, kuma duk inda yake za’a kai ga cafke shi domin ya fuskanci sharia.

Babban jami’in hukumar tsaro da kare lafiyar jama’a, na jahar Mr. Adamu Soja, ya tabbatar da batun ya kuma ce hukumar tsaron ta dakatar da Jekada, daga aiki makoni 6, da suka wuce saboda rashin zuwa wajen aiki.

Ya kara da cewa hukumar su ita ma tana neman sa ruwa a jallo kuma zai fuskanci sharia a duk lokacin da aka kai ga cafke shi.

XS
SM
MD
LG