Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga a Kan Babura Sun Kai Hari a Nijar


Sojojin Nijar yayin da suke Wani atisaye
Sojojin Nijar yayin da suke Wani atisaye

Wadansu ‘yan bidiga da ba'a san ko su waye ba sun kai hari dauke da makamai a garin Majiya Zanga da ke da'ira karkarar Allela a cikin gundumar Birni N'Konni da ke kilomita 417 daga gabascin babban Birnin Yamai.

Harin wanda aka kai a daren ranar Alhamis ya yi sanadin mutuwar mutun guda a lokacin da ‘yan bindigar su tara suka far wa yankin suka kwashe kayan masu shagunan garin suka arce.

Magajin Garin Allela da ke can tare da askarawan Nijer da ke wannan yankin sun kwarari maharan da suka tsallaka zuwa Najeriya kasancewa, wurin da a ka kai wannan harin ba nesa da iyakar ta Nijar da Najeriya yake ba.

Jama'ar garin na Majiya Zanga sun shiga zaman dardar bayan aukuwar wannan lamari, lura da cewa shi ne na farko da auku a garin nasu.

Wannan shi ya sa Magajin na Allela Malam Salifu Suley ce lalle mutane na cikin tashin hankali a garin na Magajiyar Zanga.

Wadannan garuruwa da ke kan iyaka da Najeriya na fuskantar ire - iren wannan matsalar ta rashin tsaro, inda ko a kwanakin baya wadansu ‘yan bindiga dadi sun sace wani ba'amuruke a garin Massalata da ke Nijar, inda aka tsallaka da shi Najeriya.

Abin da ya janyo musu fushin rundunar soja na musamman na Amurka wadanda suka yi kundunbala suka shiga yankin na Najeriya suka kubutar da ba’amurken.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00


Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG