Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Yi Wa Kansa Yankan Rago A Kano


Kamar yadda Mujallar Vanguard ta wallafa, a jiya talata ne wani tsoho wanda jami'an tsaron 'yan sanda suka bayyana sunan sa Hassan Ciroma mai shekaru 78, ya yanka kansa da kansa a wata mahauta da ke birnin Kano.

Lamarin da ya farau ya bar laukacin jama'ar garin cike da mamaki musamman juyayin irin dalilan da suka sa mamacin ya hallaka kansa.

Shaidun gani da ido sun ce da farko anga mutumin a wajan makeran da ke cikin mahautar da misalin tsakar rana, inda ake zargin ya sayi wukar da ya yanka kansa da ita.

Wadanda suka shaida afkuwar abin sun ce sun yi tunanin daya daga cikin mahautan da suka saba aiki a mahautar ne kamar yadda suke zuwa kowa ya kama aikinsa, abin ya ba jama'a mamaki ganin yadda kawai ya juya wukar da yake rike da ita ya yanke wuyan sa da hannun sa.

Shaidun da suke so a sakaya sunan su sun ce irin kuwwar da mamacin ya tafka ta sa yawanci mahautan cikin halin tsoro da razana.

Mai magana da yawun 'yan sandan jahar ASP Magaji Musa Majia ya fada wa mujallar Vanguard ta wayar hannu cewar a lokacin da suka sami labarin faruwar abin, sun garzaya domin kai masa dauki inda suka same shi kwance cikin jininsa, kuma sun kai shi wani asibiti mafi kusa inda ya ce ga garinku nan.

Jami'an 'yan sandan na ci gaba da bincike kamar yadda suka bayyana cewar binciken nasu zai nuna dalilan da suka haifar da afkuwar lamarin.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG