WASHINGTON D.C —
Rundunar 'yan Sandan jahar Bauchi, ta cafke wani mutun dan shekaru 35,mai suna Kabir Tukur, wanda ake zargi da kashe Auwalu Manu, dan shekaru 11, wanda yake dan , dan uwansa ne.
Kabir Tukur, dai ya tafka wannan ta'asa ne a karamar hukumar Kirfi dake cikin jahar Bauchi.
Da yake tabbatar da lamarin kakakin ;yan Sandan jahar Muhammad Haruna, ya ce Tukur, ya yaudari Auwalu ne ya yaudareshi zuwa daji inda daga bisani ya yi masa yankar Rago.
Kakakin 'yan Sandan ya kara da cewa bayan da ya kashe yaron shi sai ya yi kokarin ya kashe kansa inda ya yanki kansa a wuya amma sai ya fadi a sume inda daga bisani aka dauke su zuwa asibiti inda aka tabbatar da rasuwar Auwalu Manu, shi kuwa Kabir Tukur, yana Asabiti ana yi masa magani.