Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Soja Ya Harbi Mai Shirya Fina Finai


Mujallar Vanguard ta bada rahotanni akan harbin da wani jami'in tsaron soja da ba'a san ko wanene ba ya yi wa wani matashi mai sana'ar shirya fina finai a birnin legas yayin da yake hanyar sa ta komawa gida daga wurin shirya fim tare da abokin sa.

Lamarin ya faru tun ranar laraba, 16 ga watan Satumbar da muke ciki, kuma an garzaya da matashin zuwa wani asibiti mafi kusa da inda lamarin ya afku.

A jiya talata 22 ga watan da muke ciki ne wasu 'yan jarida suka ziyarci wanda aka yi wa harbin dake fama da jiyya a asibiti, kuma rahotanni sun nuna cewar kawo yanzu dai matashin baya iya magana sosai.

A hirar su da 'yan jaridar, matashin ya ce;

"muna kan hanyar mu ta komawa gida da misalin karfe biyu na dare, sai jami'in tsaron ya tsayar da mu, abokina ya so ya ruga saboda ya firgita amma na rike shi. koda shike kafin mu baro dakin shirya fina finan, abokin nawa ya sha tabar wiwi kuma na yi iya bakin kokarina in hana shi amma sai da ya sha.

"Na yi kokarin fadawa sojan dalilin da yasa muka yi dare amma amma ya cigaba da tuhumar mu wanda hakan ya kara razana abokin tafiyar tawa har ya zura da gudu. da naga haka nima sai na bishi da gudu, muna cikin gudn ne sai na gaji har na fadi kasa sai kawai jami'in sojan ya harbeni har saau hudu.

Na bude ido ne kawai naga kaina a asibiti da safe cikin azabar zafi da ciwo." a cewar sa.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG