A kokarin da ‘yan siyasa da hukumomi da ma gwamnati ke yi na ganin cewa ta raba matasa da zaman banza ko shiga harkokin daba, uwar gidan mataimakin shugaban kasa Mrs. Dolapo Yemi Isinbajo ta bullo da wani sabon shiri na horas da matasa da nufin samar masu aikin yi a tsakanin al'umma.
ita dai wannan cibiyar ta horas da matasa sunanta Starcorp.
Mr Opeyemi Michele shine wakilin uwargidan mataimakin shugaban kasar a lokacin kaddamar da wannan shirin da aka gudanar a unguwar Igamu dake birnin Lagos.
Akasarin matasan da aka zabo domin gudanar da wannan shirin, za a koya masu sana’o’i dabam-dabam.
Wani da aka sakaya sunansa, ya bayyana muradinsa na ganin ya mallaki kamfanin kansa, ya kuma kasance mai daukar wasu aiki ba sai ya yi dogaro ga gwamnati ba. Ya kara da cewa yana son ya ga ya sami wata sana’a duk da ilimin da yake da shi don ta haka ne zai zama mai dogoro da kansa.
Za a shafe makonni biyu ana horas da matasan sana’o’i dabam-dabam da suka hada da daukar hoto da shirya taruka dabam-dabam. Daga bisani za a shirya wannan horaswar ga mata don wannan karon maza kawai ake horaswa.
Kamar yadda za ku ji a nan, ga Babangida Jibrin da sautin rahoton.