Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gurfanar Da Masu Kokarin Kashe Theresa May A Gaban Kotu


Firayim MinistaTheresa May
Firayim MinistaTheresa May

Hukumar bincike ta sanar da zargin da akeyiwa wasu kan kule kullen kai hari ga Frayim Ministar Burtaniya Theresa May, dalilin da yasa aka gurfanar da su a gaban kotu

Wasu mutane biyu sun bayyana gaban wata Kotu a birnin London yau Laraba bisa zargin ayyukan ta’addanci, ana zarginsu da kulla makarkashiyar kashe firayin ministar kasar Burtaniyya Therasa May, a cewar jami’an gwamnatin kasar.

Jami’ai sun ce mazajen biyu sun kulla makarkashiyar yadda zasu kai harin wuka a unguwar Downing, inda gidan Firayin ministar yake.

Rahoton kulla kai harin wanda aka dakile ya bayyana ne jim kadan bayan da shugaban hukumar binciken sirrin cikin gida ta Burtaniyya Andrew Parker, yayi ma ‘yan majalisar kasar bayani kan barazanar ‘ta’addanci da kasar ke fuskanta, ya kuma sanar da ministocin kasar cewa hukumarsa ta sami nasarar bankadowa da hana kai hare-haren ta’addanci guda 9 a cikin shekarar nan.

Ya bayyanawa ministocin kulla kai harin a lokacin wani zama, koda yake dai ba a ba ‘yan jarida labarin ba sai bayan sa’o’i.

Facebook Forum

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG