Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tawagar Gwaman Borno Ta Kai Dauki Ma Tawagar Mai Kanuribe, Wanda Ya Mutu a Hatsarin Mota


Gwamnan Borno Babagana Zulum
Gwamnan Borno Babagana Zulum

Gwamnan jihar Borno Furfesa Babagana Umara Zulum ya ziyarci mahaifarsa da ke Karamar Hukumar Mafa a jihar Borno don ya sabunta rajistarsa ta APC. Bayan nan ne tawagar Mai Kanuribe ta yi hatsarin mota ya rasu.

Cikin manyan mutanen da su ka halarci wannan hidima ta gwamnan na jihar Borno, har da Mai Kanuribe na Lagos, Alhaji Mustapha Muhammad. Tawagar Mai Kanuribe din riga tawagar gwamna tashi daga wurin hidimar. A kan hanya ta yi hatsari har shi Mai da wasu mutane uku cikin tawarsa su ka rasu.

Tawagar Gwamnan ta zo ne ta tarar da hatsarin ya auku kuma ta kai dauki.

Gwamnan tare da Sanata Kashim Shettima da wasu shugabanni, sun gamu da hatsarin a kan hanyarsu ta dawowa daga Mafa kuma kamar yadda aka zata, gwamnan da wadanda ke tare da shi, sun bi gawarwakin Mai, da sauransu, zuwa ga danginsu a Maiduguri, su na masu tausaya wa dangin wadanda suka rasa rayukansu. Kuma ya halarci jana'izar.

Gwamna Zulum yana mai cewa marigayi Mai Kanuribe, shugaba ne mai son ci gaban Borno da jama'arta, ya yi tafiyarsa ta ƙarshe zuwa Mafa, don girmama gwamnatin Zulum da APC.

Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya gafarta kurakuran Mai, da wadanda suka mutu tare da shi, ya kuma shigar da su duka a Aljanna Firdausi.

Ga karin bayani daga Haruna Dauda cikin sauti:

Tawagar Gwaman Borno Ta Kai Dauki Ma Tawagar Mai Kanuribe, Wanda Ya Mutu a Hatsarin Mota
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:05 0:00


Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG