Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Jonathan Yana Son A kara Tsawon Wa'din Shugaban Kasa Da Gwamna


Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan.
Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan.

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya gabatar da shawarar cewa, a yiwa tsarin mulkin Nigeria gyara da zai kayyade wa’adin mulki shugaba dana gwamnoni zuwa wa’adi daya kurum amma kuma mai dan tsawo.

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya gabatar da shawarar cewa, a yiwa tsarin mulkin Nigeria gyara da zai kayyade wa’adin mulki shugaba dana gwamnoni zuwa wa’adi daya kurum, amma kuma mai dan tsawo.

A jiya talata shugaba Jonathan ya bada sanarwar wannan shiri, a yayinda yake fatar yin haka zai baiwa yan siyasa damar maida hankali wajen yiwa jama’an da suka zabe su aiki, maimakon maida hankali akan kokarin ganin an sake zabensu. Haka kuma shugaban yace daukan wannan mataki zai sa ayi tsimin kudin da ake kashewa wajen gudanar da zabe.

Sanarwar tasa bata fadi takamame yawan shekaru da za’a kayyade a wadi da zasu yi. Yanzu dai wa’adin mulkin shekaru hudu hudu ne aka amfani dashi, kuma sau biyu mutum zai iya tsayawa takara.

Haka kuma ya bada shawarar suma wakilan Majalisu a kara yawan shekarun wa’adinsu, amma, su suna iya neman a sake zabensu.

A cewarsa idan aka amince da wannan shawara, to ba za’a fara amfani da shirin ba, a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar, a lokacin ya kamalla wa’adin mulkinsa na yanzu.

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG