Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Jonathan Ya Rantsarda Ministoci Goma Sha Hudu.....


Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan. An dauki hoton ne ranar 8 ga watan jiya, a Majalisar dinkin Duniya.
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan. An dauki hoton ne ranar 8 ga watan jiya, a Majalisar dinkin Duniya.

Daga cikin ministocin da suka dauki rantsuwar kama aiki yau, 12 tsoffin ministoci ne, kuma zasu ci gaba da aiki a ma’aikatu da suka rike da.

Yau Asabar ce shugaban Najeriya Goodluck Jonatahn ya rantsar da sha hudu daga cikin ministocinsa, ya basu umurnin su fara aikin nan take.

Daga cikin ministocin da suka dauki rantsuwar kama aiki yau, 12 tsoffin ministoci ne, kuma zasu ci gaba da aiki a ma’aikatu da suka rike da.Sabbin biyu kuma, Mr. Jonathan yace za’a bayyana ma’aikatu da za’a tura su ranar litinin.

Masu zuba jari ciki da wajen Najeriya suna zura ido kan majalisar ministocin Mr. Jonathan, d a fatan sabuwar majalisar zata kawo sauye sauye da ake bukata ga kasar ta Afirka mafi yawan al’uma.

Cikin wadanda suka sake samun gurabunsu har da wadanda suka riki ma’aikatun stare tsaren kasa, hakar ma’adinai, sadarwa,da shari’a, da kuma ministan harkokin mai.

Shugaba Jonathan ya sake nada ministan ma’aikatar mai, Diezani Alison Maduke yau Asabar, duk da yawan suka da ta samu kan jinkiri zartas da dokar sauye sauye da aka juma ana dako a fannin makamashin kasar, da cin hanci da rashawa yayi wa katutu.

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG