WASHINGTON D.C —
Dangane da sabuwar dabi'ar nan da wasu matasa suka sa gaba watau dabi'ar shan minti wadda samari da 'yan mata ke ganin wayewar kai ce, wasu iyaye sun tofa albarkacin bakin su dangane da wannan.
Ita dai dabi'ar shan minti, samari da 'yan mata kan yi ta ne amma a boye watau cikin duhu, inda saurayi kan sa alawar minti a baki domin ya sami damar shawo kan budurwar sa ta yadda ta sakar masa jiki har su yi rayuwar tsuntsaye wadda akafi sani da kiss.
Kamar yadda zaku ji karin bayanin da iyayen suka yi, muna so ku rubuto mana irin naku ra'ayoyin a kan shafin mu na facebook wato dandalinvoafacebook.com
A saurari cikakken bayanin a nan.