Me masana suke cewa dangane da halayya da ɗabi'un matasa wadan da ke da nasaba da soyayya?
Mun tattatauna da wani kwararren masanin ilimi da halayyar ɗan'adam na jami'ar Bayero da ke Kano Dr Aminu Sabo Danbazau inda ya yi mana bayani dalla dalla akan zamantakewa da halayyyar matasa musamman yadda take tafiya da zamani, da kuma irin rawar da iyaye da al'uma ke takawa akan wannan lamari.
Da farko masanin ya yi tsokaci ne akan al'adar bahaushe wadda ya ce lallai tana cike da barazana saboda abinda ya kira kwaikwayo, ya kara da cewa kalon fina finai da hotuna da sauran su ta yanar gizo sun sa matasa na shi'awar wasu abubuwa musamman ma sutura. A takaice dai wannan yana nufin yadda mutane ke barin al'adun su su kama wasu wadanda ba nasu ba.
Sakin al'ada da kama bakuwar al'ada babbar matsala ce domin kuwa, lokaci na zuwa da komi zai canza kuma idan ba'a yi hankali ba, abin zai shafi kowa da kowa domin yara na tasowa suna kallon abin da ke faruwa, su ma haka za su kasance a rayuwar su.
Daga karshe ya bada shawarwari ga gwamnati, da al'umma da kuma iyayw musamman yadda za'a shawo kan wannan matsala.
Ku same mu a shafin mu na faceebook/dandalinvoa domin tafka muhawara.
Ga karin bayani.