Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saudiyya Za Ta Taimaka wa Najeriya Wajen Farfado Da Matatun Manta


Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, hagu, Yarima Mohammed bin Salman, dama (Hoto:Facebook/Bola Ahmed Tinubu)
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, hagu, Yarima Mohammed bin Salman, dama (Hoto:Facebook/Bola Ahmed Tinubu)

Najeriya wacce ita ce kasar da ta fi yawan arzikin mai a nahiyar Afirka na shigo da manta daga kasashen ketare saboda matatun manta uku ba sa aiki.

Gwamnatin Saudiyya ta yi alkawarin tallafa wa Najeriya wajen gyara matatun manta da ba sa aiki.

Ministan yada labarai Mohammed Idris ne ya bayyan hakan a cewar rahotanni.

Saudiyan ta yi wannan alkawari ne yayin wata ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi da Yarima Mohammed bin Salman a gefen taron koli da Saudiyya ta shirya da kasashen nahiyar Afirka.

“Saudiyya ta yi alkawari za ta saka hannun jari wajen farfado da matatun man Najeriya tare da ba da tallafin kudade don taimaka wa fannin hadahadar kudaden ketare.” In ji Idris.

Najeriya wacce ita ce kasar da ta fi yawan arzikin mai a nahiyar Afirka na shigo da manta daga kasashen ketare saboda matatun manta uku ba sa aiki.

A bara aka kaddamar da matatar man fetur ta Dangote, amma har yanzu ba ta fara aiki ba.

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG