Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Kabilanci Ya Yi Sanadin Rasa Rai A Abuja


Mukaddashin Kwamishinan 'Yan Sandan Abuja, DCP Ahmed Musa
Mukaddashin Kwamishinan 'Yan Sandan Abuja, DCP Ahmed Musa

Rikicin kabilanci ya da ya barke a unguwar Gwarinpa da ke tsakiyar birnin Abuja tsakanin Hausawa da Gwarawa ya yi sandin mutuwar mutum daya.

Rundunar ‘yan sandan Abuja babban birnin tarayyar Najeriya ta tabbatar da faruwar lamarin.

Mai magana da yawun 'yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh, cikin sanarwar da ta aikewa Muryar Amurka ta ce tun ranar Asabar ne rikicin ya faro a 3rd Avenue da ke cikin unguwar ta Gwarimpa, al'amarin da ya sa aka yi gaggawar aikewa da ‘yan sanda don samar da zaman lafiya.

Taron Lalubo Hanyar Samar Da Zaman Lafiya Kan Rikicin Kabilanci A Abuja 2
Taron Lalubo Hanyar Samar Da Zaman Lafiya Kan Rikicin Kabilanci A Abuja 2

Wasu mutane biyu sun sami mummunan rauni, wanda bayan kai su asibiti dayan ya cika a daidai lokacin da likitoci ke kokarin ceto ransa sakamakon raunuka da ya samu.

Mai rikon mukamin kwamishinan ‘yan sandan birnin Abuja, DCP Ahmed Musa, tuni ya yi ganawar gaggawa da shugabannin Gwarawa da Hausawa a ofishinsa don lalubo hanyar samar da zaman lafiya.

Taron Lalubo Hanyar Samar Da Zaman Lafiya Kan Rikicin Kabilanci A Abuja 1
Taron Lalubo Hanyar Samar Da Zaman Lafiya Kan Rikicin Kabilanci A Abuja 1

'Yan sandan wadanda a halin yanzu suka kaddamar da bincike don gano musabbabin faruwar rikicin sun ce sun kama wasu da ake zargi, kana an jibge karin jami'an tsaro da ke sintirin tabbatar da tsaro a yankin.

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG