Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Neymar Na Neman Doke Pogba A Fagen Taka Leda


Kungiyar kwallon kafa ta PSG dake kasar Paris ta saka zunzurutun kudi har fam miliyan £180 kimani dalar Amurka miliyan $223 domin sayan dan wasan gaba na kasar Brazil mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona mai suna Neymar.
Ta bakin mai kungiyar ta PSG Nasser Al-Khelaifa ya ce yana matukar bukatar dan wasan a kungiyarsa a kakar wasan bana Wanda idan wannan cinikin ya kasance to zai zamo babu dan wasan kwallon kafa da yakai shi tsada a duniyar kwallon kafa.
A yanzu haka dan wasan tsakiya na Manchester United, Paul Pogba, shi yafi kowa tsada a duniyar tamola kan kudi fam miliyan £89 wanda Manchester ta saya daga Kingiyar Juventus a farkon kakar wasan bana.

Sai dai wata majiyar na cewa kungiyarsa ta Barcelona taki amincewa da tayin da PSG tayi akan Neymar, inda take cewa zata kara daukaka darajansa ta hanyar kara masa kudi domin ya cigaba da zama a kungiyar ta Barcelona inda tace tana da tabbacin Neymar bazai bar Barcelona a yanzu ba sai dai har yanzu ba aji ta bakin dan wasan ba.

Ita kuwa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dake ingila tace zata ba da dan wasanta Eden Hazard wa kungiyar Juventus domin mallakan mai tsaron baya na kungiyar juventus mai suna Leonardo Bonucci.

XS
SM
MD
LG