Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NATO Zata Girke Sojoji A Wasu Kasashen Gabashin Turai da Suka Hada da Poland


 Jens Stoltenberg babban sakataren NATO
Jens Stoltenberg babban sakataren NATO

A wani yunkurin kungiyar NATO da ana iya ganinsa tamkar yiwa Rasha hannunka mai sanda ne, kungiyar zata girke sojoji a kasashen Poland da Estonia da Latvia da Lithuania, kasashen da kasar Rasha ta fi yiwa barazana

Sakatare-Janar din kungiyar kawancen NATO, Jens Stoltenberg ya fadi jiya Litini cewa NATO za ta amince ta girke bataliyoyi hudu na kasa da kasa a Poland da Estonia da Latvia da Lithuania - wadanda su ne kasashen da su ka fi fuskantar barazana daga Rasha.

"Wannan zai aika da sako dalla-dalla na cewa NATO fa a shirye ta ke ta kare duk wata kawarta," a cewar Stoltenbeg a gabanin taron Ministocin Tsaron kasashen da ke cikin kungiyar ta NATO wanda za a fara yau Talata a Brussels, inda ake sa ran jami'ai za su rattaba hannu kan shirin girke sojojin. Stoltenberg ya ce bataliyoyin za su rinka karba-karba ne karkashin jagorancin kwamandojin NATO.

Tattaunawar na aukuwa ne gabanin babban taron NATO da za a yi a Warsaw, kasar Poland a watan Yuli.

Wasu shugabannin kasashen Baltic irinsu Latvia da Lithuania da Estonia, su na cikin fargaba saboda sojojin da NATO ke shirin girkewa ba su da yawan da za su iya sa Rasha ta yi shakkar kai duk wani hari.

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG