Akalla mutane biyar ne suka rasa rayukansu, bayan da aka samu zaizayar kasa a Indonesia.
Bayanai sun ce wasu mutane 15 sun bata a wani kauyen da ke kan Tsibirin Java.
Wani kakakin, hukumar da ke sa ido kan aukuwar wani bala’i, ya ce, lamarin ya faru ne a yau Alhamis a tsibirin da ke Gundumar Brebes a tsakiyar yankin Java, a daidai lokacin da manoma ke aiki a gonakinsu na shinkafa.
Zaizayara kasar ta auku ne a cewar mazauna yankin, bayan da aka kwashe kwanaki da dama ana tafka ruwan sama, wanda hakan ya sa kasar tsaunukan da ke zagaye da yankin ta yi laushi.
Tuni aka baza sojoji da ‘yan sanda domin neman wadanda bala’in ya rutsa da su, inda suke amfani da fatanyu da kuma hannayensu wajen tonon kasa, saboda laka ta hana a yi amfani da manyan na'urori.
Facebook Forum