Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Me Yasa Wasu Iyaye Ke Yi Ma 'Ya'yan Su Auren Dole


A yau dandalin VOA ya tattauna da wasu matasa ne akan auren dole, wato makasudan dalilan da ke sa wasu iyaye ke yi ma 'ya'yan su auren dole.

Da farko mun fara jin ta bakin Sama'ila Bima Mai Gombawa, daga nan sai malam Adamu BCGA shima ya bayyana nasa ra'ayin.

Mai Gombawa ya fara fadar ne inda yayi bayanin cewa a nasa ra'ayin, tabarbarewar tarbiyar 'ya'ya na daya daga ciki, ya kara da cewar babu yadda za'a yi uba na ganin diyar sa ko dansa na kokarin lalacewa ya rabuda ita ko shi.

Musammana ma 'ya mace, wasu iyayen sun gwammace su aurar da ita ta ko wanne hali domin su huce takaicin irin abubuwan da take aikatawa a gida.

Wasu iyayen kuma, sukan aurar da 'ya'yan nasu ne a sakamakon neman abin duniya, ya kara da cewar talauci na sa wasu iyaye su fara neman inda zasu aurar da 'ya'yan su mussamman ga masu hannu da shuni, iyaye da dama sun aurar da 'ya'yan su saboda kudi.

Daga karshe ya bayyana cewar akwai illoli da dama dake tattare da auren dole, yawanci wasu mata matasa kan gudu ne har ma sai kaga daga karshe sun fara karuwanci, kokuma su fara tunanin hallaka juna.

Saurari Cikaken Shirin.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG