Masu kada kuri’a a Rasha sun amince a yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska ta yadda Shugaba Vladamir Putin zai samu damar yiwuwar ci gaba da kasancewa kan kujerar mulki har shekarar 2036.
Amma zaben jin ra’ayoyin da aka kwashe tsawon mako guda ana yi wanda aka kammala ranar Laraba 1 ga watan Yuli na cike da rahotannin an matsa wa masu kada kuri’a lamba, da kuma wasu kurakurai.
Yayin da aka kirga kuri’u daga gundumomi kashi 3 cikin 4, masu kada kuri’a kashi 77.6 cikin 100 ne suka amince a yi kwaskwarima a kundin tsarin mulkin, a cewar jami’an zabe.
Wani gagarumin kamfe na farfaganda da aka yi da kuma gazawar da ‘yan adawa suka yi wajen hada kai su kalubalanci kudurin ya taimaka wa Putin samun sakamakon da ya ke bukata, amma ta yiwu sakamakon ya zama kalubale ga mukamin na sa daga karshe saboda hanyoyin da aka yi amfani da su wajen habbaka zaben jin ra’ayoyin.
Kwaskwarimar da za ta ba Putin dama ya sake neman wa’adin shugabanci na shekara 6 har sau biyu, a shekarar 2024 da 2030, na daga cikin canje-canjen da za a yi a kundin da kuma haramta auren jinsi daya, da yin Imani ga Allah a matsayin muhimmin abu da kuma sanya dokokin Rasha gaban abubuwan da kasa-da-kasa suka dauka da muhimmanci.
Facebook Forum