Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manoma Da Makiyaya A Janhuriyar Nijar Sun Gana Don Magance Matsalolinsu


A birnin Konni dake jihar Tahoua a Janhuriyar Nijar an bude wani taron muhawara da safiyar Alhamis domin neman hanyar dinke barakar dake tsakanin manoma da makiyaya a karshen lokacin damina a Nijar.

Kungiyar makiyaya da ake kira AMPEN a takaice, a Janhuriyar Nijar, da hukumomin Jihar Tahoua sun shirya wannan taron ne don tattauna matsalolin da ake samu tsakanin makiyaya da manoma.

Dakta Usman Sumaila, Magajin garin birnin Konni yace wannan taron da aka shirya faduwa ce ta zo daidai da zama. Saboda yankin na fuskantar rikici tsakanin makiyaya da manoma duk lokacin da damina ta zo karshe. Ya kuma ce a kullum suna cikin fargaba, har sai lokacin da manoma suka kwashe amfanin gonarsu.

An dai shirya wannan taron ne don neman hanyar samun zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya, da kuma ilimintar da al’ummomin biyu akan dokar kasa, a cewar malam Abdalla, shugaban kungiyar makiyayan da ta shirya wannan taron.

Mataimakin gwamnan jihar Tahoua, da shugabannin gargajiya da kungiyoyi dabam dabam ne suka halarci taron mahawarar.

Ga karin bayani cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00

Facebook Forum

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG