Hukumomin kula da lafiya na kasar Nigeria, na yiwa Mahajatta gwaji a babban filin jirgin sama na Murtala Muhammad a birnin Ikko, kafin su tashi zuwa kasar Saudi Arebiya, a wani kokarin neman shawo kan yaduwar kwayar cutar Ebola.
Maniyyatan Aikin Hajjin Bana da Aka Yiwa Gwajin Cutar Ebola, filin jirgin sama na Murtala Muhammad a Birnin Ikko, 22 ga Satumba, 2014

9
Jami’an kula da lafiyar matafiya na duba fasfo kafin su yi amfani da ma’aunin zafin jiki su yiwa Mahajjata gwajin cutar Ebola.

10
Mahajjata na tsaye a wani sansanin alhazai su na jira a yi mu su gwajin cutar Ebola kafin su shiga jirgin saman zuwa Saudiyya, a ranar goma sha takwas ga watan satumba shekarar dubu biyu da goma sha hudu.