Darektan hukumar da take kula da zirga zirgan jiragen saman fasinja na kasar Alfred Mtilatila, yace galibin shirin na gwaji yana samun goyon bayan asusun tallafawa yara na Majalisar Dinkin Duniya ko MDD a takaice, wato UNICEF.
A karkashin shirin, jiragen zasu yi jigilar jini da ya bushe wand aka dauka daga yara da aka haifa da cutar kanjamau ko sida.
A cikin watan Maris ne Malawi ta sami nasarar kammala shirin gwajin aiki da jiragen a yanki mai fadin kilomita 10, daga wata cibiyar kiwon lafiya zuwa babban asibiti dake birnin kasar Lilongwe.
Ahalin yanzu kasar tana amfani da babura ko motocin jigilar marasa lafiya ne wajen yin wannan zirga zirga. Amma hukumomin kiwon lafiya suka ce tsadar mai da kuma rashin kyawun hanyoyi suna janyo jinkiri mai yawa wajen kai wadannan muhiman bukatun kiwon lafiya.